'Yan siyasa sun damu da yadda zasu kamo bakin zaren kare rayukan al'umma da kan taru a layukan jefa kuri'a.
Ko sabon shugaban kasa mai jiran gado Janar Buhari ya bada tabbacin tunkarar matsalar tsaro da zara sun kama madafin iko watan gobe. Ya yi alkawarin kawo karshen rubar da jinin jama'a ba bisa shari'a ba.
Shugaban ma'aikatan Janar Buhari wato Kanal Hamid Ali ya nuna ta'azibin yadda 'yan Boko Haram ke yin barazana ga lamuran zabe.Yace 'yan ta'adan basu amince da tarayyar Najeriya ba. Suna yakar kasar domin su kafa tasu daular. Maganar zabe bata cikin huruminsu.
Daya daga cikin 'yan takaran zabe a inuwar APC Muhammad Inuwa Yahaya ya nuna damuwa da yadda 'yanbindigan ke addabar arewa maso gabas musamman kauyen Kashere inda suka yi batakashi da jami'an tsaro da ya firgita al'umma. Yace idan aka yi la'akari sai a ga cewa batun Boko Haram da gangan ne. Ba'a taba jin Boko Haram a Gombe ba sai ranar da mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro ya jefa Gombe cikin jihohin Boko Haram. Tun daga lokacin 'yan Boko Haram din suka raba takardun kada a yi zabe. Shin me ya hada Boko Haram da zabe a Najeriya.
Ya kira jami'an tsaro su yi aikinsu na gaskiya. Su killace duk inda ake zaton za'a samu matsala. Su tabbatar an yi zabe lafiya, zabe kuma mai inganci.
Shi ma gwamnan jihar Dankwabo ya shawarci jama'a su dinga zuba ido da hada kai da jami'an tsaro warin magance kalubalen.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.