Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Yan Najeriya Dauke da Tsintsiya da Ruwa


Matasa na Murna.
Matasa na Murna.

‘Yan Najeriya maza da mata yara da manya sun fito kan hanyoyi domin nuna farin cikin su dangane da nasarar da Muhammadu Buhari ya samu ta zama sabon zababben shugaban kasa.

A yayin da Janar Buhari ya doke abokin takararsa na jam’iyar PDP, Goodluck Jonathan a babban zaben kasa da aka gudanar ranar asabar 28 ga watan Maris da ya gabata.

A wani rahoton wakilin sashin Hausa na muryar Amurka Abdulwahab Mohammad ya bayyan yadda jama’a da dama a jahohin Bauchi da Gombe ke tururuwa akan tituna suna rawa da kuma bushe-bushe.

Wasu kuma suna dauke da ruwa da tsintsiya suna zubawa a kasa suna wankewa. Wani daga cikin mutanen dake kade-kade da raye-rayen ya bayyana dalilinsa da kuma fatan su ga wannan sabuwar gwamnatin,

“Ina mai matukar farin ciki kwarai musamman yadda kowa da kowa hatta mata da kananan yara duk sun fito domin taya wannan sabuwar gwamnati murna, kuma muna farin ciki kwarai domin zai kawo mana sauyi.”

Fatan jama’a da dama a wannan lokaci shine, kawo karshen zubar da jinin da ake fama dashi dangane da hare haren kungiyar Boko Haram mai tada kayar baya a wasu jahohin Arewa maso gabashin Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG