Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Blinken Ya Sake Kai Ziyara Gabas Ta Tsakiya Akan Batun Yankin Gaza Da Falasdinawa


Israel/Palestinians/US - Blinken
Israel/Palestinians/US - Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Saudiyya a yau Litinin a ziyararsa ta biyar a yankin tun bayan barkewar yaki a yankin Gaza, yana fatan ci gaba da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma shiri bayan yakin da dakile tashe-tashen hankula a yankin.

WASHINGTON, D. C .- Amma a dukkan bangarorin uku yana fuskantar manyan kalubale.

Egypt/US/Mideast - Blinken
Egypt/US/Mideast - Blinken

Hamas da Isra'ila suna takun saka a bainar jama'a game da muhimman abubuwan da za a iya cimma. Isra'ila ta yi watsi da kiraye-kirayen da Amurka ta yi na neman hanyar samun kasar Falasdinu, kuma kawayen Iran masu fafutuka a yankin ba su nuna alamun ja da baya ba duk da hare-haren da Amurka ke kaiwa ba.

A Gaza kuma, Hamas ta fara sake bullowa a wasu yankunan da aka fi samun barna bayan da sojojin Isra'ila suka ja da baya, lamarin da ke nuni da cewa babban burin Isra'ila na murkushe kungiyar yana nan daram. Hotunan bidiyo daga wurare guda suna nuna rugurgujewar dukiyoyi, tare da kuma lalacewar kusan gidaje.

ISRAEL/PALESTINIANS - BLINKEN
ISRAEL/PALESTINIANS - BLINKEN

Ana sa ran Blinken zai gana da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman. Jami'an Saudiyya sun ce har yanzu masarautar tana sha'awar daidaita huldar da ke tsakaninta da Isra'ila a wata yarjejeniya mai muhimmanci, amma sai dai idan akwai ingantaccen tsari na samar da kasar Falasdinu.

Sai dai duk da tsanmanin, da kyar hakan ya yiwu haka a yayin da har yanzu ake ci gaba da gwabza fada a yankin na Gaza, inda aka kai gawarwakin mutane 113 asibitoci a cikin sa'o'i 24 da suka gabata kadai, a cewar ma'aikatar lafiya a yankin da Hamas ke mulki. Ma’aikatar kuma ta ce wasu mutane 205 kuma sun jikkata.

Israel/Palestinians/US - Blinken
Israel/Palestinians/US - Blinken

Kasashen Amurka, Qatar da Masar sun gabatar da wani kudiri na tsagaita wuta na makonni da dama tare da sakin sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

Sai dai Hamas, wadda har yanzu ba ta mayar da martani ga wannan shawara ba, ta ce ba za ta sake sakin fursunonin ba har sai Isra'ila ta kawo karshen farmakin da take kaiwa. Ana sa ran mayakan za su bukaci a sako dubunnan fursunonin Falasdinawan a madadin haka, amma bukatun da Netanyahu ya yi watsi da shi a bainar jama'a.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG