Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hare-haren Isra’ila Sun Halaka Mutane A Wata Makaranta


Yadda harin Isra'ila ya haskaka sararin samaniya
Yadda harin Isra'ila ya haskaka sararin samaniya

Makarantar wacce ake kira Al Fakhoura da ke Gundumar Jabalia na dauke da dubban mutane a lokacin da aka kai harin kamar yadda Juliette Touma, Darekta a hukumar ‘yan gudun hijirar ta fadawa Reuters.

Wasu hare-haren sama da Isra’ila ta kai a yankin Zirin Gaza a ranar Asabar sun halaka mutane da dama yayin da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya gana da ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa a Jordan inda ake neman maslaha kan rikicin da ya dabaibaye yankinsu.

Hare-haren saman na Isra’ila sun yi daidai da wasu yankuna ne da aka ba al’umar Gaza umarnin su nemi mafaka a cewar Falasdinawa.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya, ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa harin da aka kai kan wata makaranta da Majalisar ta Dinkin Duniya ke kula da ita a arewacin Gaza, ya halaka akalla mutum 15 tare da jikkata wasu da dama.

Makarantar wacce ake kira Al Fakhoura da ke Gundumar Jabalia na dauke da dubban mutane a lokacin da aka kai harin kamar yadda Juliette Touma, Darekta a hukumar ‘yan gudun hijirar ta fadawa Reuters.

A cewar Touma daga cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai yara kanana, amma hukumar ba ta kai ga tantance iya adadin wadanda suka mutu ba.

Firaiminista Benjamin Netanyau ya ce Isra’ila za ta ci gaba da kai hare-haren kuma ba za ta amince da wata matsayar dakatar da bude wuta ba idan babu batun sako Isra’ilawan da aka kama a cikinta.

Kungiyar Hamas wacce Amurka ta ayyana a matsayin ta ‘yan ta’adda ta kama yahudawa 230 sannan ta kashe mutum 1,400 a harin da ta kai a ranar bakwi ga watan Oktoba.

A gefe guda kuma, magoya bayan Falasdinawa sun gudanar da zanga-zanga a biranen London, Berlin, Paris, Ankara, Istanbul da nan birnin Washington D.C. inda suka yi kira da a cimma matsayar dakatar da bude wuta a Gaza.

A London, hotunan talbijin sun nuna dandazon mutane da suka yi bore na zaman dirshan, inda suka toshe wasu yankunan tsakiyar birnin, kafin daga bisani su nausa zuwa wasu yankunan birnin.

Dubban mutane ne suka yi tattaki a titunan birnin Washington D.C. dauke da tutocin Falasdinua suna rera wakokin dora laifi akan Biden a kusa da ginin Freedom Plaza da ba shi da nisa da Fadar White House.

A tsakiyar birnin Paris na kasar Faransa kuwa, dubban mutane ne suka yi tattaki suna kira da a cimma matsayar dakatar da bude wuta dauke da kwalaye masu sakonnin neman kawo karshen rikicin.

A birnin Berlin na kasar Jamus kuwa, masu zanga zangar sun kasance dauke da tutotcin Falasdinu, inda su ma suka yi kira da a dakatar da bude wutar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG