Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Blinken Ya Kara Jaddada Goyon Bayan Amurka Ga Isra’ila Tare Da Yin Kira A Kare Fararen Hula A Gaza


Antony Blinken
Antony Blinken

Daruruwan dubban Falasdinawa ne suka rasa gidajensu sanadiyyar hare-haren saman da Isra’ila take kai wa kan Hamas a matsayin martanin harin da ta kai wa Isra’ilan.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce batun hana yaduwar fadan Isra’ila da Hamas, shi ne ya zamanto jigo a tattaunawar da suka yi da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da majalisar da kasar ta kafa a Tel Aviv don kula da sha’anin yaki.

Bayan tattaunawar, Blinken ya fadawa manema labarai matakan da ya zama dole a dauka domin ganin an kaucewa aukuwar irin harin da mayakan Hamas suka kai a ranar 7 ga watan Oktoba a kuma tabbatar da kyautatuwar makomar al’umomin Isra’ila da Falasdinu.

Kungiyar Hamas da Amurka ta ayyana a matsayin ta ‘yan ta’adda ta yi garkuwa da yahudawa 230 ta kuma halaka 1,400 a harin da ta kai.

Blinken ya kuma nanata goyon bayan Amurka ga Isra’ila na daukan matakan kare kanta, amma ya kuma ja hankalin hukumomin kasar da a kare fararen hula a yankin na Gaza.

“Akwai bukatar a kare rayukan Falasdinawa fararen hula, mun bayyana cewa, yayin da Isra’ila take kare kanta a yakin da take yi na kawar da mayakan Hamas, duba yadda ake tunkarar lamarin na da muhimmanci.” In ji Blinken.

Daruruwan dubban Falasdinawa ne suka rasa gidajensu sanadiyyar hare-haren saman da Isra’ila take kai wa kan Hamas a martanin harin da ta kai wa Isra’ilan.

Ma’aikatar lafiya a yankin gaza da hamas ke iko da shi ta fada a ranar alhamis cewa adadin mutanen da suka mutu ya haura dubu tara

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG