Shugaban Amurka Joe Biden zai yi balaguro zuwa New Orleans a mako mai zuwa domin ganawa da iyalan mutanen harin da aka kai da mota wanda ya hallaka mutane 14 ya rutsa dasu, kamar yadda fadar White House ta sanar a yau Juma’a.
A Litinin mai zuwa, shugaban da mai dakinsa Jill za su taya iyalai da al’ummar garin da al’amarin ya shafa alhinin harin da aka kai ranar 1 ga watan Janairun da muke ciki tare da ganawa da jami’an da suke wurin,” a cewar sanarwar da fadar White House ta fitar.
Birnin wanda ke kudancin Amurka ya fada cikin firgici a ranar bikin sabuwar shekara sa’ilin da wani tsohon sojan Amurka, Shamsud-Din Jabbar da ke biyayya ga kungiyar masu ikirarin jihadi ta ISIS, ya yi amfani da motar akori kura wajen hallakawa tare da raunata masu murnar shigowar sabuwar shekarar a wani wurin holewa da ke French Quarter ta yankin.
Ba’a daina zubar da jini ba har saida ‘yan sanda suka harbe wanda ake zargin a wata musayar wuta.
Mutumin ya kuma birne bama-bamai 2 kirar gida a kewayen birnin dukka dai ba su tashi ba, a cewar hukumomin.
Dandalin Mu Tattauna