Hukumar tsaro ta FBI a Amurka, ta ce harin da wani direba ya kai wa masu bikin sabuwar shekara a birnin New Orleans ba na ta'addanci ba ne.
"Wannan ba harin ta'addanci ba ne", a cewar jami'ar hukumar yayin da ta ke bayani bayan karbe ragamar bincike kan harin.
Abin da ya saba wa kalaman magajin garin, LaToya Cantrell, wanda ya ayyana harin a matsayin harin ta'addanci.
A yau Laraba ne hukumomi a birnin New Orleans na Amurka suka bayyana cewa mutane 10 sun mutu kuma fiye da 30 sun jikkata lokacin da wata mota ta afka cikin dandazon jama'ar dake kan titin Bourbon.
A yau Laraba hukumomin birnin New Orleans suka sanar da mutuwar mutane 10 da jikkatar wasu 30 sakamakon al'amarin da ya rutsa da mutane da dama, inda wata mota ta afka cikin dandazon jama'a akan titunan Canal da Bourbon.
Kafafen yada labaran yankin sun bada rahoton cewa al'amarin ya afku ne da misalin karfe 3 da mintuna 15 na asubahin yau agogon yankin.
Birnin, shahararren wurin yawon bude idanu da shakatawa ne a Unguwar Faransawa da ke da kimanin mutane 360, 000 a jihar Louisiana dake kudancin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna