Zababben Shugaban Amurka Donald Trump ya alakanta mummunan harin motar da aka kai kan dandazon masu bikin sabuwar shekara a garin New Orleans a yau Laraba da kwararar bakin haure ta barauniyar hanya-batun da ya mamaye nasarar zaben da ya samu.
"Zancen da nake yi na cewa masu laifin dake katarowa sun fi illa a kan wadanda muke dasu a cikin kasa ya tabbata,"
Trump ya wallafa hakan a shafinsa na sada zumunta gabanin a fayyace bayanan mutumin da ya kai harin a matsayin ba-Amurke mai suna Shamsud-Din Jabbar, wanda kuma ke dauke da tutar kungiyar ISIS ta masu ikirarin jihadi ta duniya.
Haka kuma Trump ya yi ikirarin cewa yawaitar aikata laifi a kasar ya kai mizanin da ba'a taba gani ba."
Hukumomi a birnin New Orleans na Amurka sun bayyana cewa mutane 10 suka rasa rayukansu kuma fiye da 30 suka jikkata lokacin da wata mota ta afka cikin dandazon jama'ar da ke kan titin Bourbon.
Mutumin da ya afka da motar ba-Amurke ne mai suna Shamsud-Din Jabbar.
Jabbar na dauke ne da tutar kungiyar masu ikirarin jihadi ta duniya, ISIS, a cewar hukumar FBI mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka.
Dandalin Mu Tattauna