Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mace-Macen New Orleans Sun Yi Matukar Bakanta Ran Fafaroma - Fadar Vatican


A yau Alhamis, Fafaroma Francis ya bayyana ta'aziyarsa ga babban limamin katolika na New Orleans akan harin da aka kai birnin dake Amurka wanda ya hallaka akalla mutane 15, a cikin sakon da fadarsa ta Vatican ta aike.

A yau Alhamis, Fafaroma Francis ya bayyana ta'aziyarsa ga babban limamin katolika na New Orleans akan harin da aka kai birnin dake Amurka wanda ya hallaka akalla mutane 15, a cikin sakon da fadarsa ta Vatican ta aike.

"Mai Alfarma Fafaroma Francis ya yi matukar bakin ciki da samun labarin asarar rayuka da jikkatan da harin ya sabbaba," kamar yadda sakataren harkokin wajen kasar Vatican, Cardinal Pietro Parolin ya rubuta a wasikar daya aikewa Archbishop Gregory Aymond, inda ya kara da cewar, Fafaroman ya yi addu'ar samun waraka ga wadanda suka jikkata da juriya ga wadanda aka. yiwa rashi."

Wani direba, Shamsud-Din Jabbar, ya afka da motar akori kura cikin dandazon jama'ar da ke bikin shigowar sabuwar shekara a garin New Orleans na na jahar Louisina ta Amurka, sannan ya kuma bude wuta, inda ya kashe mutane 15 tare da jikkata wasu fiye da 35.

Hukumar FBI mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka ta ce, tana gudanar da bincike kan harin da ta kira a matsayin harin ta'addanci, kuma ta yi imani cewa direban ba shi kadai ya yi aika-aikar ba.

Alethea Duncan, mataimakiyar wakili ta musamman mai kula da ofishin FBI a New Orleans, a wani taron manema labarai ta ce, Ofishin yana binciken daruruwan mutanen da ake zargi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG