Mutumin da ya afka da motar akori kura cikin dandazon jama'ar dake bikin shigowar sabuwar shekara a garin New Orleans a yau Laraba ba-Amurke ne mai suna Shamsud-Din Jabbar.
Jabbar na dauke ne da tutar kungiyar masu ikirarin jihadi ta duniya, ISIS, a cewar hukumar FBI mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka.
"An tsinci tutar kungiyar ISIS a cikin motar, kuma FBI na kokarin tantance kungiyoyin da mutumin ke yiwa aiki da kuma alakarsa da sauran kungiyoyin 'yan ta'adda," kamar yadda FBI ta bayyana a cikin wata sanarwa.
Wanda ake zargin ya hallaka akalla mutane 10 tare da jikkata 30 gabanin a harbe shi a musayar wuta da 'yan sanda.
An tsinci bama-baman da basu tashi ba hadin gida a cikin motarsa a kewayen unguwar Faransawa ta birnin New Orleans, a cewar FBI.
Dandalin Mu Tattauna