"Harin ta'addanci ya afkawa birnin New Orleans, da Faransawa ke matukar kauna," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.
"Tunaninmu na tare da iyalan mutanen da harin ya rutsa dasu da wadanda suka jikkata, dama al'ummar Amurka, da muke tarayya dasu a alhini."
Hukumomi a birnin New Orleans na Amurka sun bayyana cewa mutane 10 suka rasa rayukansu kuma fiye da 30 suka jikkata lokacin da wata mota ta afka cikin dandazon jama'ar da ke kan titin Bourbon.
Mutumin da ya afka da motar ba-Amurke ne mai suna Shamsud-Din Jabbar.
Jabbar na dauke ne da tutar kungiyar masu ikirarin jihadi ta duniya, ISIS, a cewar hukumar FBI mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka.
Dandalin Mu Tattauna