Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BAUCHI: Ma'aikatan Kananan Hukumomi Sun Shiga Zanga zanga


Masu zanga zanga
Masu zanga zanga

Masu zanga zangar a garin Bauchi babban birnin jihar sun zargi babban sakataren ma'aikatar kananan hukumomi da shirya makarkashiya saboda wai baya son gwamnan jihar ne.

Shugabannin ma'aikatan kananan hukumomi sun nuna kin amincewarsu da cire masu wani kaso cikin albashinsu ko alawus.

Shugabannin sun zargi Alhaji Hudu Yusuf Ari babban sakataren ma'aikatar kananan hukummi da zama tushen rikicin. Suna cewa shi ne umalubaisan yukurin rage masu albashi da kuma rashin biyansu na har watanni uku. Wai Alhaji Ari ne ya shirya zabtare masu kudi.

Kwamred Shehu Isa shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomin jihar yace sun zo ne su yi magan akan albashinsu. Yace sun samu bayanai cewa za'a zabtare wani bangaren albashinsu kana a biyasu sauran. Wai an cire wan bangare wanda ba za'a biya ba amma za'a biya sauran.

Yace sun tuntubi babban sakataren ma'aikatar dake kula da kananan hukumomi Alhaji Ari wanda ya tabbatar da hakan. Biyo bayan abun da babban sakataren ya tabbatar ma'aikatan sun zauna sun kuma yanke shawar kin karbar abun da za'a biyasu muddin bai cika ba. Su ba zasu karbi albashin ba muddin bai cika ba.

Ga rahoton Abdulwahab Mohammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG