Janar Buhari ya gayawa jama'a cewa ba zai bari a cigaba da yin kwanciyar nagirbi da dukiyar kasa ba a gwamnatinsa.
Yace a matsayinsa na zababben shugaban kasa "na yi maku alkawari ba zan ci amana ba da kuma sani na ba za'a ci amana ba in kyale" Yayi addu'ar Allah ya kawo saukin wannan sabuwar tafiya da zai yi da kasar. To saidai yace zata yi wuya domin barna an riga an yita. Ya kara da cewa "to amma na yi imani tunda kowa ya ji a cikinshi" mutane su yi damara.
Da ya juya akan zaben gwamnoni Janar Buhari ya shawarci jama'a su zabi 'yan takaran APC a jihohin Adamawa da Taraba. Yace samun gwamnatin tarayya ba zai yi ma'ana ba idan basu da gwamnoni da 'yan majalisun dokoki da zasu taimaka.
Kafin Janar Buhari ya zarce zuwa Gombe sai da ya karbi wasu kusoshin jam'iyyar PDP da suka canza sheka zuwa APC. Yace ya yi murna da karbar gogaggun 'yan siyasa.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.