Yayin da ake ta shirye shiryen rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya, wani sabon batun da ya taso kuma shine batun shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai, inda shugabannin jam'iyar APC dake yankin Gabas maso Arewacin kasar yayi maganar cewa lokaci lokaci fa yayi.
A wata sanarwa da 'yan jam'iyar suka fitar, sun bukaci cewa lokaci yayi da yakamata a ba yankin Arewa maso Gashin Najeriya jagorancin majalisar dattawa kokuma ta wakilai. A wata hira da wakilin sashin Hausa Ibrahim Abdul'aziz, Mr Bidi Lawal wanda shine mataimakin shugaban jam'iyar na kasa a yankin Arewa maso Gabas ya bayyana dalilansu kamar haka.
"Yamma maso kudu suke da mataimakin shugaban kasa dan haka yakamata su hakura su barmana guda, kudu maso kudancin Najeriya basu da kowa a APC, kuma an maida abin kamar sarauta a yankin arewa ta sakiyar Najeriya domin sun saba rike mukamin shugaban majalisa, Kuma munfi su kuri'a."
Alfanun wannan kuzera a Arewa maso Gabashin Najeriya kamar yadda 'yar takarar gwamnan jaha a karkashin jam'iyar APC ta jahar taraba sanata A'isha Jummai Alhasan ta bayyana shine, "munkawo APC a dukkan jahohi shidda na Arewa maso Gabashin Najeriya kuma muna sa ran cewar zamu kawo gwamnoni shiddan, sai dai bamu taba rike kujerar kakaki ba dan haka muna fatan za'a bamu."
Wannan wannan maganganu sun taso ne daf da lokacin da shugaban Najeriya mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara a jahar Adamawa da jahar Gombe domin karbar wasu 'yan jam'iyar PDP masu canza sheka wadanda suka hada da wasu tsofaffin gwamnoni.