Rashin kamanta gaskiya, adalci, mutunta jama'a da rashin bin tsari wajen gudanar da harkokin jam'iyyar musamman lokacin tankade da rairaya na fitar da 'yan takara da kuma zaben shugabannin jam'iyyar su ne suka kasheta.
Wasu da suke kusa da fadar shugaban kasa Goodluck Jonthan su ne suka lissafa dalilan, lamarin da ya sa wasu manyan 'yan jam'iyyar suka fice suka shiga APC da wasu jam'iyyu.
Alhaji Isa Mafindi Tafidan Muri, mataimakin kakakin kemfen din shugaba Jonathan, ya ambaci manyan jam'iyyar da suka fice. Yace wanene zai ce Turakin Adamawa baya cikin turban kafa jam'iyyar PDP. Haka ma Kawu Baraje da Musa Kwankwaso. Yace tun lokacin da gwamnoni bakwai suka fice daga jam'iyyar yace abun zai kaisu ga halaka. Yace saboda haka duk abun da ya samu jam'iyyarsu sun fi kowa sani kuma su ne suka lalata jam'iyyarsu.
Shi ma shugaban jam'iyyar na jihar Adamawa Joel Madaki yace zaben da ya wuce PDP taba nema ba yadda ya kamata. Yace su ne PDP din amma basu nema yadda yakamata ba.
Umar Ardo daya daga cikin 'yan takarar gwamna a zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP a jihar Adamawa har garzayawa kotu yayi sabili da abun da yace jam'iyyar ta yi mashi.Umar Ardo ya bayyana hujjoji uku da suka jawowa jam'iyyar asara. Na daya PDP bata yi rawar gani ba domin ta yi zalunci a harkan gwamnati saboda sace-sace da aka yi. Na biyu jam'iyyar da kanta dauki dora tayi-ta dora wadanda basu cancanta ba kan mukamai.
Ga rahoton Sanusi Adamu.