Matakin ba zai rasa nasaba da mahimmancin gwamnoni wajen karfafa jam'iyya daga tushe da daga darajar 'yan siyasa.
Barrister Abubakar Bauchi na APC na ganin targaden da PDP ta samu ba mai gyaruwa ba ne. Yace dama abun da take gadara dashi gwamnatin tarayya ce. To gwamnatin ta kubuce mata.Tana gadara da hukumomin tsaro suma sun kubuce mata.Sabon shugaba Janar Muhammad Buhari shi ne yake da iko dasu yanzu da zara ya dare kan mulki.
Yace yanzu babu wata barazana da PDP zata iya yi. Yace jam'iyyar ta sha turzaza sarakuna suna tara hakimai da dagatai suna fada masu tilas su sa a zabi PDP.
Sabon dan majalisar wakilai Umaru Barambu yana ganin ba laifi ba ne irin tsoffin 'yan PDP da suka koma APC su ci gajiyar guguwar Buhari. Shi mai taimakawa gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo kan labaru Junaidu Abubakar yace ko Buhari yace a yi APC tsaf ba zai sauya kirkin wasu 'yan PDP ba.Yace nasu Buharin a jihar Gombe shi ne Talban Gombe.
Saidai matasan 'yan siyasa nada ra'ayi daban. Ali Kumo na APC yace shure-shure baya hana mutuwa. PDP ta kare. Amma Abdullahi Ali Kano cewa ya yi PDP ta yi shekaru 16 tana mulki dole ta sabawa wasu. Duk abun da ake yi yanzu na 'yan adawa ne da suke son su nuna zasu fi PDP iyawa. Yace lokaci zai nuna.
Ga rahoton Adamu El-Hikaya.