Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Zaben Gwamnoni: 'Yan PDP Sun Rabu Gida Biyu


Yayinda kakakin PDP Oliseh Metuh ke buga kirjin cewa PDP zata bada mamaki a zaben gwamnoni da za'a yi a karshen wannan makon wasu 'yan PDP a Abuja suna ganin jam'iyyar ba zata kai labari gida ba

Duk da rashin nasarar da jam'iyyar PDP ta samu a zaben shugaban kasa, kakakinta Oliseh Metuh yayi ikirarin cewa PDP zata bada mamaki a zaben gwamnoni da za'a yi.

To saidai matsayin 'yan PDP dake Abuja fadar gwamnatin Najeriya ya rabe gida biyu. Wasu na cewa jam'iyyar ba zata yi rawar gani a zaben gwamnonin ba. Wasu kuma 'yan takarar PDP din na ikirarin su ne masu irin dabi'un da Buhari ke bukata.

Misali, mataimakin kakakin kefen na shugaba Jonathan Isa Tafida Mafindi yace a jiharsa Taraba, Aisha Alhassan 'yar takaran jam'iyyar APC zai zaba. Yace duk jam'iyyar da ta yi zaben fitarda dan takara ita zasu yi. Yace inda kuma jam'iyya ta fitarda dan takara ta dorawa mutane dan takara dole "to sai a kuma tilasta masu su zabeshi"-inji Mafindi. Yace APC ce ta yi zaben fitarda dan takara yayinda ita PDP ta yi nadi. Yace wanene zai kai matsayin siyasa kamarsa ya je kuma ya zabi wanda aka nada? Mafindi yace hakan ba zai yiwu ba.

Shi kuma dan takarar PDP na jihar Yobe Adamu Maina Waziri yace dabi'arsa irin ta Buhari ce.Yace za'a samu anfani idan aka samu mutane masu akida irin ta Buhari kuma masu kuzari irin nashi da masu jajircewa irin nashi su zama shugabanni a jihohi.

A nasa bangaren dan takaran APC Inuwa Yahaya na jihar Gombe na ganin kaucewa muradun kashin kai ne zai haskawa mutane gwadaben zaben sahihan 'yan takara da kaucewa yaudara. Yace gaf da zaben shugaban kasa aka makawa jihar Gombe Boko Haram. Ban da haka gwamnati ta sa sojoji sun kewaye gidan Sanata Haruna Goje wai domin kada ya fita ya je ya yiwa APC aiki. Boko Haram yakamata sojoji su je su yaka ba dan siyasa ba. Duk matakan an dauka ne domin a dakile APC kana a gina karya. Amma idan gaskiya ta fito dole karya ta gudu.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG