Tafida Isa Mafindi Yariman Muri wanda kuma shi ne mataimakin kakakin kemfen din shugaba Goodluck Jonathan yace a Najeriya an gama zabe lafiya. Yace Najeriya ce ta ci zabe. Najeriya ce aka sa a gaba.
Yace dukansu sun dawo sun bi wanda ya ci zabe. Shi ne shugaban da za'a rantsar dashi. Suna tsammanin yadda aka zabeshi zai rike duk 'yan kasar gaba daya ba tare da nuna banbanci ba.
Shi ma Faruk Ahmed Gusau mai goyon bayan shugaba Jonathan yace jam'iyyun APC da PDP Danjuma ne da Danjummai saboda haka a hada kan Najeriya yadda shi shugaban kasa mai ci ke so. Yace a daina murnar nasara amma godiya ga Ubangiji ita ce martabar tafiya. Kada a yi anfani da nasarar da aka samu a ce za'a azabtar da wanda bai goyi baya ba. Allah bai yiwo mu daidai ba tun ba ma Najeriya ba inda ya zubo kabilu daban daban.
Sanata Dajo Abubakar Batsari yace shugaba Jonathan ya yi rawar gani. Ya ba sabon shugaban kasa shawarar karrama shugaba Jonathan. Ya nada Jonathan a matsayin jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya. Ya kira Jonathan Mandela na biyu. Mandela ne yake kan mulki ya sauka ya bada. Ya kuma kira Janar Buhari ya tuna wannan sabon mulkin da zai soma ba na soja ba ne, na dimokradiya ne.
Ga rahoton Medina Dauda.