APC reshen jihar Neja ta ce ta bankado wani shiri da PDP ke yi domin tafka magudi a zaben da za'a gudanar ranar asabar mai zuwa.
To sai dai tuni jam'iyyar PDP ta nesa kanta daga zargin. Jami'in yada labarai na APC a jihar Neja, Mr. Jonathan Batsa ya shaidawa taron manema labarai irin abubuwan da suka ce sun bankado.
Ya ce sun shirya kananan hukumomi guda bakwai inda PDP za ta yi magudin zabe ta aika sakamakon zabe wanda ba na hukumar zabe ba ne.
Haka kuma ya yi zargin cewa an ba kowane jami'in INEC nera miliyan guda.
Amma kakakin jam'iyyar PDP Alhaji Hassan Saba ya mayarda martani ya na mai cewa basu da wannan niyyar kuma ba za su yi ba.
Ya kuma kara da cewa Idan da suna da wannan niyyar da an gani a zaben baya. Saboda haka sun yi imani da ikon Allah zai basu nasara a zaben.
Duk da wannan zargin da musanta shi hukumar zabe ta ce ta yi shiri tsaf ta gudanar da zaben.
Madaki Wase jami'in kula da jama'a na hukumar ya ce basu da masaniya akan korafin APC.
Ga karin bayani a rahoton Mustapha Nasiru Batsari.