A cigaba da taimakawa gajiyayyu da ake yi albarkacin watan Ramadan, Kungiyar Izalatul bid’a Wa’iqamatis Sunnah ta Kasa ta raba ma marayu da sauran mabukata wajen 700 kayan tallafi don sun kammala azumi cikin natsuwa su kuma yi Sallah cikin kwanciyar hankali.
Wakilinmu a Naija Mustapha Nasiru Batsari y ace kayan da Izala ta raba ya kai na Naira miliyan 10. Ya ruwaito shugaban Majalisar Malaman Izala shiyyar Naija Sheikh Aliyu Adarawa na cewa dalilin daukar wannan matakin shi ne Allah ya yi alkawarin taimaka ma duk wanda ya taimaki mabukata. Ya ce ya kamata duk wanda bai son a ki taimakon ‘ya’yansa bayan ya mutu shi ma ya taimaki marayu.
Shi kuwa wani Sheihin malamin kungiyar a matakin kasa, Sheikh Abubakar Giro Argungu cewa ya yi taimakon marayu, hasali ma na daya daga cikin ayyukan da kungiyar ta sa gaba. Y ace an kafa Izala ne saboda Alkur’ani da Hadisi; kuma Alkur’ani da Hadisai su ke sa a aikata ayyuka masu kyau kuma na lada kamar wa’azi da taimaka ma marayu da dai sauransu.
Wata daga cikin wadanda su ka amfana mai suna Umma Ibrahim, mai ‘ya’ya 6 da ubansu ya mutu, ta ce lallai kam sun samu taimako mai karfafa gyuwa, da su ka hada da shinkafa da zani da kudin dinki.