A yau Litinin, masu tattaunawa a bangaren Iran da wakilan manyan kasashen duniya ciki har da na Amurka sun dukufa wajen ganin an kammala ganawar watanni 18 da aka kwashe ana yi domin cimma matsaya kan takaddamar nukiliyar Iran.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya ce yana da yakinin za a cimma matsaya guda, ko da ike, ya ce akwai batutuwa da suka rage, kuma ba zai yi alkwarin za a cimma yarjejeniya a karshen yau Litinin ba.
A jiya Lahadi, mahalarta taron suka kyan-kyasa cewa bangarorin biyu suna daf da cimma matsaya.
Yau 13 ga watan Yuli, na daga cikin jerin ranakun da bangarorin biyu suka shatawa kansu a matsayin wa’adin karshe na kulla yarjejeniya.
Sai dai, wani jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran, Alireza Miryousefi, ya ce babu batun ko za a kara tsawaita wa’adin.