Kungiyar Izala a Najeriya tace ta yaba da samun nasarar cafke wadanda ake zargin da kai harin boma-bomai a garin Jos da kuma Zaria ta jihar Kaduna da jamian tsaron kasar suka ce sunyi.
A dai-dai lokacin da yake rufe tafsir na wannan shekarar a garin Minna mataimakin shugaban malaman Izalar a Najeriya Sheik Yusuf Sambo Rigachukum, yace yana baiwa hukumomin Najeriya shawarar matsar wadanda aka kama domin Karin samun bayani.
‘’Tunda dai anyi laifi kuma ga masu laifi an kama inda gwamnatin Najeriya zata yi adalci ya kamata ta takura wadannan mutanen kar ta sake su ta samu labari cikakke daga wajen su, suwa ke sasu wadannan ayyuka, bayan an gano wadanda suke sa su sannan da su wadanda suka sasu da wadanda sukayi aikin duka gwamnati ta yanke musu hukuncin kissa, bayan ta yanke musu hukuncin kissa kuma gwamnati ta kwace makama dake hannun su, kuma gwamnati tasa a bincika duk wanda yake rike da makami ba bisa kaida ba to lallai ne ai ainihin amshe makamin nan’’.
To amma a daya gefen kuma Sheik Yusuf Sambo Rigachukum ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta biya diyyar wadanda aka kashe iyalan su a wannan harin domin rage musu zafi.
‘’Kuma dinbin al’ummar da aka kashe a wajen karatu a ainihin jos da wadanda aka kashe a kasuwa da wadanda aka kashe a Zaria to hakki ne gwamnatin kasar Najeriya ta biya diyyar kudaden wadannan mutanen da aka kashe aba magadan su diyyar kudaden nan, wajibi ne gwamnati tayi wannan to in anyi hakan kaga an hukunta duk bangarorin to daga yau zaka ga an kame hannun mutane daga wannan aikin’’.
A halin da ake ciki kuma rundunar yan sandar jihar Niger tace ta samu Karin motocin yin sintiri a dajin kan iyakar jihar Niger da Kaduna domin fatattakar yan fashi da masu satar jamaa.Da suka addabi yankin inji kakakin rundunar yan sandar jihar Mr Bala El-Kana.
‘’Mun samu Karin motocin faturo, samu guda 15 daga Abuja, mun kara guda 5 sun zama 20 kenan, shi kuma mai girma kwamishina ya samo Mashina don akwai inda motoci basu iya shiga, an samo mashina a shiga cikin dajin nan gaba daya a fatattake su’’
Kakakin yan sandar jihar Niger Mr Bala El-Kana.
Ga Mustafa Nasir Batsarida Karin bayani.