Tsari na baya bayan nan shi ne hana barace barace a gefen hanya da tallace tallace.
To amma wasu da abun ya shafa sun ce sam dokar ba zata taba zama karbuwa ba a wurinsu saboda ta wannan hanya ce kadai suke ciyar da kansu da iyalansu da kuma samun biyan bukata..
Ranar Asabar da ta wuce nakasassu a Kaduna sun yi gungu domin nuna rashin jin dadinsu game da dokar suna cewa babu gudu babu ja da baya daga barace baracen da suke yi. Malam Muntari Sale mai magana da yawun kungiyar nakasassu ta jihar Kaduna yace gwamna El-Rufai ya sa ana kamasu ba tare da basu abincin da zasu ci ba ko aikin da zasu.
Malam Muntari Sale ya rantse da Allah cewa ba zasu bar barace barace a Kaduna ba sai dai idan za'a hallakasu gaba daya.
To saidai gwamnatin jihar tace duk da tirjewar nakasassu matsayin gwamnati kokarin tsarkake tsaron jihar ne da samun tsarin da zai anfani kowa. Samuel Aruwa mai magana da yawun gwamnatin jihar ya sake jaddada dalilin hana barace barace da tallace tallace. Yace harakar tsaro ta sa gwamnati daukan matakin. Sun yi hakan ne domin tsaurara matakan tsaro da kuma kare rayukan mutane..
Ga rahoton Isa Lawal Ikara.