Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Addini Keda Nauyin kawo Daidaituwar Al’umma Cikin Kasa


Gwamnati ta kalubalanci shugabannin addinin musulunci dana kirista

‘’Ku shugabannin addini na musulmi dana kirista kune ALLAH ya dankawa kune wakilan ALLAH, kune zaku ja mu zuwa wuta kune zaku jamu zuwa aljanna .Yau a Adamawa kuna nan ace wai Minchika Kirista da Musulmi basu gaisuwa da juna, kuna nanga coci yafi dubu Masallaci yafi dubu ace kasuwa a Minchika ya zama kasuwa biyu, musulmi suci yau kirista suci gobe ku hada kanku maza-maza kusan yadda zamu fuskanci Minchika domin a samu zamantakewan lafiya babu yadda za ayi addini, addini ya raba mu a Adamawa karya ne karya ne’’.

Shugaban maaikatan jihar Adamawa Alhaji Abba Jimeta Kenan ke kalubalantar shugabannin addinin musulunci dana kirista sailin gayyatar liyafar cin abincin buda baki da Alhaji Muhammadu Jibrila Bindowa yayi musu a gidan gwamnati, Kiristoci da Musulmai mazauna garin garin Michika dake arewacin jihar Adamawa sun share sama da shekara daya suna zaman doya da manja lamarin da ya haddasa kyama da rashin mutunta juna wanda yakai ga raba ranakun cin kasuwar su.

Mabiya addinin kirista na cin kasuwar su ne a ranar asabar, yayin da mabiya addinin Musulunci ke cin nasu kasuwan a ranar lahadi.

Da kuma aka tambayi shugaban kungiyar kiristoci na kasa reshen jihar Adamawa Bishop Michael Moses da takwaransa Sakataren gamayyar majiisar kungiyoyin addinin musulunci reshenn jihar Adamawa Alhaji Ismail Modibbo Umar ina gaskiyar cewa su malamam addini ke cusa wa mabiyan sun a kiyayya da kuma kyama.

‘’Sunana Bishop Micheal Moses ni kuma CAN chairman ne na Adamawa state ba gaskiya a ciki sabili da mu shugabannin addini aikin da aka bamu kiran Ubangiji gare muyi waazin salama ga wayan da kuma suke ganin Kaman malaman addini musammam ma ko ace fastoci haka da sauran su su suke iza wannan abun ba dai-dai bane.Dan daima har zamu shiga a ciki damu zamu shiga ne a madadin masu bada shawarwari da sulhu da kuma wadanda suke son ayi zaman lafiya’’

‘’Sunana Ismaila Moddibo Umar Sakatare janar na Muslim kansil na jihar Adamawa don Addinai da ake dasu a duniya duka ba addinai da suke kusa da juna kamar addinin Musulunci da addinin kirista, A gaskiya shekaru sunkai muyi kokari mu tattauna musammam Musulmi da kirista da suke zama a Michika domin muga mun shawo kan matsalar da take faruwa tsakanin su musammam abinda ya shafi cin kasuwa guda biyu, rashin jituwa, rashin muamulla, da sauran ire-iren su wanda ya zamana idan dai ance kasar Michika , na san da cewa karamar hukuma guda da yace , dole suna da Sarki daya, idan gwamnati bata raba wannan ba, to bamu ga hujjan za a yi rarrabiya akan abinda ya shafi kasuwa da sauran ire-iren suba’’.

Ga Sanusi Adamu da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG