A cikin watan Yuli ne Jamhuriyar Nijar ta zama mamban ECOWAS ta baya bayan nan da aka yi juyin mulki a lokacin da sojoji masu gadin fadar shugaban kasar suka tsare shugaba Mohammed Bazoum tare da kafa abin da suka kira gwamnatin rikon kwarya, daya daga cikin jerin gwamantin da aka hambarar a yankin Sahel a yammacin Afirka.
A taron kolin da aka yi ranar Lahadi a Abuja babban birnin Najeriya, ECOWAS ta yanke shawarar kafa wani kwamiti na shugabannin kasashen Togo, Saliyo da Benin, domin tattaunawa da gwamnatin mulkin sojan Nijar, don cimma matsaya kan "shata tsarin mika mulki na gajeren lokaci" da kuma yin aiki "cikin gaggauta domin maido da tsarin dimokaradiya".
"A bisa ga sakamakon tattaunawar kwamitin shugabannin kasashen da gwamnatin mulkin sojan Nijar ne, hukumomi za su duba yiwuwar sassauta takunkumin da aka kakabawa Nijar," in ji ECOWAS.
Kungiyar yankin ta kara da cewa, idan har gwamnatin mulkin sojin Nijar ta gaza bada hadin kai ga sakamakon da aka cimma, za a ci gaba da tabbatar da takunkumin da aka sanya mata, har da yiwuwar amfani da karfi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, wanda ke zaman shugaban ECOWAS, tun da farko ya ce kamata ya yi kungiyar ta yi kokarin sake zama da kasashen yankin da ke karkashin mulkin soja tare da tallafa musu wajen ganin sun cimma muradinsu na komawa ga tafarkin dimokaradiya cikin gajeren lokaci.
A saurari rahoton Umar Farouk Musa daga Abuja:
Dandalin Mu Tattauna