Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Tana Zargin Faransa Da Kisan Kiyashi a Aljeriya


PM Turkiyya Recep Tayyip Erdogan
PM Turkiyya Recep Tayyip Erdogan

Turkiyya tana zargin Faransa da aikata “kisan kare dangi” a Aljeriya, fiyeda shekaru 60 da suka wuce.

Turkiyya tana zargin Faransa da aikata “kisan kare dangi” a Aljeriya, fiyeda shekaru 60 da suka wuce.

Frayin Ministan kasar Recep Tayyip Erdogan ne yayi zargin jumma’an nan, kwana daya bayan da wakilan majalisar dokokin Faransa suka zartas kuduri da zai haramta furtawa a bainar jama’a cewa, ba a yi wa Armeniyawa kisan kare dangi zamanin mulkin Ottoman a Turkiyya, kusan karni guda da ya wuce.

Armeniyawa sun ce sojojin Turkiyya sun kashe jinsinsu milyan daya da rabi, lokacin yakin Duniya na daya, zamanin daular Ottoman, lamari da masana tarihi suka ce shine halaka mutane mafi muni da aka yi karni na ashirin. Kodashike Turkiyya ta yarda anyi hasarar rayuka matuka, tace an kara gishiri, sabo da yawansu bai kai ace ya kai “kisan kiyashi ba”. Turkiyya tace mace- macen sun auku ne sakamakon yaki.

Da yake magana Jumma’a kan dokar, PM Erdogan yayi zargin Faransa ta kashe kashi 15 na al’umar Aljeriya lokacin tana yi wa kasar mulkin mallaka, laifi data fara a 1945 inji Turkiyya.

Ranar Alhamis majalisar wakilai ta Faransa ta amince da dokar, wacce tace duk wadda ya musanta sojoji turkawa a zamanin Ottoman a lokacin yakin Duniya na daya a 1915, basu yi wa Armeniyawa kisan kare dangi ba, zai fuskanci tarar dala dubu $60,000 da kuma daurin shekara daya a gidan yari.

Yanzu dokar an turata ga majalisar dattijai ta Faransa domin neman amincewa.

Mr. Erdogan ya Fada yau jumma’a cewa zartas da wan nan doka alamace a fili yadda nuna banbancin launin fata, kyama da kiyayya da ake nunawa musulmi ya kai wani mizani a Faransa da kuma turai.

Sabo wa nan rikici,Turkiyya ta janye jakadan ta daga Faransa, kuma ta hana sojojin ruwan Faransa shiga ruwayen kasar ta. Haka kuma ta hana jiragen yakin Faransa shiga sararin samaniyar Turkiyya.

XS
SM
MD
LG