‘Yan bindiga da yawa dauke da manyan makamai ne suka kai harin a kan kauyukan guda biyu a ranar Lahadi.
A yayin harin da ya dauki tsawon sa’o’i 4, ‘yan bindigar sun harbe mutune 20 tare da raunata wasu biyu, suka kuma yi wa wata motar ‘yan sandan sintiri da ta je kai dauki wurin kwanton bauna, inda ‘yan bindigar suka kashe jami’an ‘yan sanda 4 da jami’an tsaron sa kai na jihar.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Abubakar Sadiq, ya bayyana cewa rundunar na aiki da duk masu ruwa da tsaki a jihar domin dakile sake aukuwar lamarin tare da kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki.
Ya kara da cewa rundunar ta kuma tura karin kwararrun jami’ai da kayan aiki zuwa yankin.
“A ranar kuma, da misalin karfe 3 na safe, an samu kiran wayar gaggawa a hedkwatar jami’an tsaron shiyya ta garin Kankara, kan cewa ‘yan bindiga dauke da manyan makamai a kan babura sun yi harbe-harbe, sun kuma kai hari a kauyen Gidan Baki duk a karamar hukumar Kankara, inda suka kashe wasu mazauna kauyen, a cewar Sadiq.
“A yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Gidan Baki, sai jami’an suka gano cewa, a kauyen Gidan Boka ta ‘Yar Goje aka kai harin, kuma ba tare da bata lokaci ba sai suka juya, suka nufi wajen da lamarin ya faru.
Ya kara da cewa “Da isarsu kauyen Kurmeji ta ‘Yar goje, sai ‘yan bindigar suka yi wa tawagar jami’an kwanton bauna, inda aka yi musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar."
Dandalin Mu Tattauna