Wannan kuma na zuwa ne ranar da gwamnatin jihar ke kaddamar da yaye jami'an bayar da tsaro ga al'umma da ta horas.
Lamarin rashi tsaro a Najeriya na ci gaba da yin kwan gaba kwan baya, domin matakan da ake dauka sun kasa hana 'yan bindiga aika aikar su.
A jihar Sakoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, a daidai lokacin da gwamanatin jihar ke kaddamar da jami'an tsaron al'umma, 'yan bindiga ne suka kutsa kai cikin wani gari da ake kira Gidan Bakuso a karamar hukumar Gada da ke gabashin jihar suka sace dalibai almajirai da adadin su bai kasa goma sha biyar ba.
Liman Abubakar wanda shi ne malamin makarantar allon da aka sace almajiran, ya ce 'yan bindigar sun shigo cikin tsakiyar gari sun kamo wata mata sai suka biyo ta wajen makarantarsa, inda almajiransa suka ji kukan wannan mata da suka kamo.
Ya ce daliban nasa suna da yawa sai suka tashi su kai ta shiga cikin dakunansu yayin da ‘yan bingar suka tusa keyar wasu da dama daga cikin almajiran.
Dan majalisar jiha mai wakiltar yankin Kabiru Dauda ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya ce ana kan kokarin daukar matakan da suka dace don maganin wannan matsalar da makamantan ta a duk fadin jihar.
Duk a ranar daya 'yan bindiga sun kai wani hari a kamarar hukumar Isa, inda suka kashe wasu mutane ciki har da hakimin kauyen.
Wakilin al'ummar a majalisar dokoki ta jiha, Habibu Halilu Modaci, ya ce 'yan ta'addar suna cin karen su ba babbaka ne saboda jami'an da aka tura su fatattake su, ba su samu damar iya kawarda su ba.
Da yake gwamnatin Sokoto ta bi sahun takwarorinta, kamar Katsina da Zamfara wajen samar da jami'an tsaron al'umma dan majalisar jihar ya ce akwai bukatar ayi da gaske.
A yayin hada wannan rahoto dai gwamnonin jihohin Kebbi, Zamfara, Katsina, Bauchi da tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro Janar Ali Gusau, mai ritaya suna a Sokoto, domin kaddamar da jami'an tsaron al'umma kuma daren washe garin ranar ne 'yan bindiga suka yi wannan aika-aika.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna