Da yammacin ranar Lahadi ne wasu ‘yan bindiga da ke kan babura suka afkawa garin Yargoje da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, kamar yadda wani mazaunin garin, Hassan Ya’u, ya bayyana.
"Sun harbe mutane kai-tsaye, inda suka kashe fiye da 50, ciki har da kanina," kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.
Ya kara da cewa an yi garkuwa da mutanen kauyen da ba a san adadinsu ba tare da wawushe kadarori.
Wani mazaunin garin, Abdullahi Yunusa Kankara, shi ma ya ce da kyar ya tsallake rijiya da baya, kuma harin ya ci gaba da faruwa har zuwa safiyar ranar Litinin. "Garinmu ya rikide ya zama yankin mutuwa, kusan kowane gida a kauyen ya fada cikin wannan hari."
Kankara ya kara da cewa "A halin yanzu muna gudanar da kidayar jama'a domin tantance adadin mutanen da aka sace, an kuma gano wasu gawarwakin da safiyar yau."
Hukumomin ‘yan sandan Katsina ba su amsa bukatar jin ta bakinsu ba.
Ana ci gaba da kai hare-hare a yankunan karkara da kuma yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a arewacin Najeriya, yankin da rikicin 'yan ta’adda da aka kwashe shekaru 15 ana yi a yankin arewa maso gabas da kuma rikicin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiyar kasar ya yi kamari.
Dandalin Mu Tattauna