Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Mr. Ban Ki-moon yace ya kamata a bada fifiko da muhimmanci wajen tabattarda cewa kasashen Afrika suna samun isasshiyar wutar lantarki da sauran fasahun makamashi don ci gaban al’ummarsu. Da yake magana a ranar Lahadi, ranar da aka kebe ta zama “Ranar Inganta Harakokin Masana’antu a Afrika”, Magatakardan na MDD yace rashin wutar lantarki yana janyo cikas da ja-baya sosai a kokarin da ake na rayad da kasashen na Afrika. Mr. Ban ya nuna bakin cikin ganin cewa akwai mutanen Afrika masu yawan milyan 600 da basa da ingantacciyar hanyar samun makamashi.
Majalisar dinkin duniya na son mutanen kasashen Afrika su sami ingantacciyar wutar lantarki