Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gorbachev yace anyi magudin zabe a Rasha

Tsohon shugaban Rasha Mikhail Gorbachev.
Tsohon shugaban Rasha Mikhail Gorbachev.

Tsohon shugaban kasar Rasha Mikhail Gorbachev ya bukaci a soke zaben wakilan majalisar dokokin kasar a kuma kaddamar da sabo. Mr Gorbachev yace sakamakon bai nuna abin da mutane suka zaba ba.Ya kara da cewa tilas ne hukumomin kasar su yarda an tafka magudi.

Dan shekara 80 da haifuwa, Mr. Gorbachev ya fada yau laraba cewa yin kunnen kashi da bukatar jama’a zai zubda mutuncin hukuma a idanun jama’a, kuma ya lalata al’amari.

‘Yan hamayya da masu sa ido na kasa da kasa duk sunyi zargin cewa an tafka mummunar magudi da keta wasu dokokin zabe.

Hukumomin kasar sun baza jami’an‘Yansanda dubu hamsin da jirage masu saukar ungulu da suka rufa musu baya akan titunan birnin Moscow domin hana zanga zanga kan zargin magudin zabe a wuni na uku.

A halin da ake ciki kuma, Rasha ta yiwa kungiyar kawancen tsaro ta NATO kashedin cewa girka garkuwa daga makamai masu linzami a turai zai janyo gasar jibge makamai.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG