Hukumomin kungiyar Tarayyar Afirka sun ce mai yiwuwa kasar Ethiopia ta shiga cikin fadan da ake gwabzawa da mayakan al-Shabab da ke Somaliya, wanda wannan wata hobbasa da ka iya zama wani sabon fagen dagan yakar wannan kungiya mai alaka da al-Qaida.
Jami’an gwamnatin Ethiopia sun ce har yanzu ba a yanke shawara ta karshe ba ta shigarta cikin babbar gamayyar soji da nufin kawar da al-Shabab kwatakwata. To amman mai magana da yawun ma’aikatar Harkokin Waje Dina Mufti y ace Ethiopia za ta shiga a dama da ita.
Dina y ace mai yiwuwa ranar jumma’a mai zuwa a bayar da sanarwar niyyar Ethiopia ta shiga gamayyar, bayan wani taron kungiyar cigaban kasashe 6 ko IGAD a takaice.
Ana dai kyamar sojojin Ethiopia a Somaliya, inda mutane da dama ke masu ganin masu tsanani, a yayin da su ka abka cikin kasar daga 2006 zuwa 2009.