Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kama dan Gaddafi a kudancin Libiya


Seif al-Islam Gaddafi kenan cikin jirgi a Zintan
Seif al-Islam Gaddafi kenan cikin jirgi a Zintan

Jami’an gwamnatin Libiya sun ce Dakarun Abu Bakr Sidiq da ke

Jami’an gwamnatin Libiya sun ce Dakarun Abu Bakr Sidiq da ke birnin Zintan sun kama Seif al-Islam Gaddafi, dan tsohon shugaban Libiya marigayi Moammar Gaddafi.

Kwamandan mayakan na Zintan Beshir al-Atrib ya fadi a wani taron manema labarai da ya kira a birnin Tripoli jiya Asabar cewa an kama Seif al-Islam Gaddafi da wasu masu taimaka masa su uku a kusa da garin Obari da ke kudancin Libiya a yayin da yak e kokarin tserewa zuwa kasar Nijar.

Tuni kasar Nijar ta bayar da mafaka ga dan’uwansa Saadi, to amman Shugaban kasar, Mahammadu Issoufou, ya fadi a makon jiya cewa ba a yanke shawara ba kan a bin da za a yi idan Seif al-Islam ya roki mafaka.

Al-Atrib ya nuna fatan kama Seif al-Islam Gaddafi zai zama babban al’amari ga ‘yan dukkannin ‘yan Libiya kuma makomar Libiya za ta yi kyau kuma hadin kan kasa zai zama burin kowa da kowa.

An yi ta katse taron manema labaran akai akai saboda sowar ‘yan kallon da su ka rinka tafi suna cewa “Allahu Akbar” da babbar murya.

Ministan Cikin Gidan Libiya na wuccin gadi Mohammed al-Alaqi ya gaya wa gidan Talabijin din al-Arabiya cewa an tafi da Seif al-Islam zuwa Zintan bayan kama shin. Da farko al-Alaqi ya nuna cewar za a mika Seif al-Islam ne ga Kotun Manyan Laifuka ta kasa da kasa (ICC) da ke birnin Hague, wadda tun dama ta bayar da sammacin kama shi, to amman daga baya ya jaddada cewa a Libiya ne za a mar shari’a, bisa ga ka’idojin kasa da kasa.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG