Gwamnan yace yayi imani jami'an tsaron Najeriya da na waje suna taimakawa kuma za'a cimma nasara wajen samun yaran. A kan jinkirtawa wajen bin sawun wadanda suka sace yaran da fara bincike gadan gadan lokacin da abun ya farau sai gwamnan yace wakilinmu ya mika tambayar ga gwamnatin tarayya domin sha'anin tsaro na hannun gwamnatin tarayya. Gudunmawar da zasu iya bayarwa daga jihar shi ne bada labarin abun da suka ji da kuma taimakawa da motoci ko man fetur da kuma abubuwan yau da kullum. Amma gwamnan yayi imani za'a gano yaran cikin koshin lafiya.
Gwamnan yace shi zai fitar da batun siyasa a wanna lamarin. Zai bar wasu su yi siyasar. Amma a matsayinsa na uban 'ya'yan da aka sace babu batun siyasa. Abun dake damunsa kuma suka sa a gaba shi ne a samo yaran cikin koshin lafiya. Sauran kuma a yi nan gaba.
Dangane da yadda harkar tsaro ta shafi cigaban aikin raya kasa sai gwamnan wanda ya hada da rantsuwa yace ya shafesu matuka. Yace da Borno ita ce cibiyar kasuwancin arewa ba Kano ba domin shi yayi aiki a banki kuma ya san abun da ake ciki. Kasuwar Kano ma ta dogara ne da kasuwar Borno ne. Daga Borno kaya na zuwa Zaire har Afirka Ta Tsakiya da Sudan da Kamaru da sauransu. Amma tabarbarewar tsaro ta kashe kasuwar fiye da yadda ake tsammani. Ta tsiyartar da mutanensa ta kawo talaucin karfi da yaji. Amma yayi imani Allah zai dawo da zaman lafiya.
Gwamna Ibrahim Shettima yace suna da tarihi na shekaru dubu kuma duk matsalar da suka shiga sun fita. Haka ma wannan ta yanzu zata wuce. Allah ba zai cigaba da ajiye bawansa cikin mawuyacin hali ba dindindin. Duk abun duniya mai karewa ne.
Ga karin bayani.