Mamallakin matatar man fetur ta Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewar lokaci ya yi da gwamnatin Najeriya za ta dakatar da biyan tallafi a kan man fetur.
Yayin wata hira da mujallar Bloomberg a jiya litinin, Dangote yace biyan tallafi akan man zai janyo gwamnati ta kashe kudaden da bai kamata ta kashe ba,” don haka akwai bukatar ta dakatar da shi.
Attajirin dan kasuwar ya jaddada cewar gwamnatin Shugaba Tinubu ba za ta iya dorewa da biyan tallafin man fetur din ba.
"Ina ga lokaci ya yi da Najeriya za ta janye tallafin mai baki daya domin dukkannin ƙasashe sun daina biyan shi.
"Batun tallafin fetur magana ce babba. Idan ka bayar da tallafi a kan wani abu, wasu sai su rika kara yawan abun domin su samu karin kudade sannan sai nauyin ya ƙare a kan gwamnati. Zai fi dacewa a daina biya baki ɗaya."
Dangote ya nuna matukar jin dadinsa da kammala aikin da mutane da yawa ke shakkun cewa zai iya yin nasara, yana mai cewa wannan gagarumin nasara ce ga kamfaninsu da Najeriya.
Matatar man da aka kwashe kusan shekaru goma ana ginata, ta fuskanci matsaloli da dama da suka hada da rikice-rikicen al'ummar yankin da kuma tsaikon da gwamnatocin jihohi suka haifar. Duk da wannan cikas, tawagar Dangote ta jajirce, inda ta dauki nauyin aikin injiniya, saye da kuma ’yan kwangilar gine-gine da kansu don ganin an kammala aikin kamar yadda attajirin ya bayyana.
A kan batun tallafin man fetur, Dangote ya goyi bayan matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na cire tallafin mai, yana mai jaddada rashin dorewar al’adar. Ya kara da cewa an dade ana amfani da tallafin, wanda hakan ya sa gwamnati ta biya fiye da abinda ake bukata.
Alhaji Aliko Dangote yace, matatar mai na Dangote ta shirya tsaf don taimakawa wajen samar da gaskiya a kan ainihin yadda ake amfani da man fetur a Najeriya da kuma rage matsin tattalin arzikin kasashen waje ta hanyar samar da kayayyaki a cikin gida.
Dangote ya yi imanin cewa matatar tasa za ta daidaita darajar Naira ta Najeriya da kuma amfanar tattalin arziki wajen kara bunkasa shi.
A cikin hirar Dangote ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa aiwatar da matakan kirkire-kirkire domin karfafa rawar da matatar take takawa a bangaren makamashin kasar.
Idan ba’a manta ba, gwamnati ta amince za ta sayar da danyen man fetur ga matatar Dangote a Naira, wanda zai ba da damar yin hada-hadar kudaden cikin gida, wanda hakan zai rage matsin lamba a kan Naira da kuma rage dogaron da kasar ke yi na musayar kudaden waje kamar yadda masana tattalin arziki da dama suka yi ittifaqi.
Yusha’u Aliyu da ke Abuja, kwararren mai sharhi ne kan tattalin arziki kuma ya yi wa Muryar Amurka karin haske kan wannan al’amari inda ya bayyana cewa:
“Duk da kokarin da Dangote ya yi na samar da wannan matatar mai mafi girma a Afirka wanda tabbas abin a jinjina masa ne, amma kuma dole a sani cewa wannan bayani na Dangote bai wuce bayanin dan kasuwa da yake so ya gudanar da harkokin kasuwancin sa cikin sauki ba” inji Malam Yusha’u.
Har ila yau, masanin ya kara da cewa a wannan batu kowani bangare yana da muradu da yake so a biya masa, gwamnati tana son karin kudin shiga wanda cire tallafin ya samar da ribanya kudin shiga na gwamnati daga biliyoyi zuwa tiriliyoyin Naira da ake rabawa jihohi.
Su kuma al’umma babu abinda suke bukata illa wadatar mai da kuma samar da shi cikin farashi mai kyau da zasu iya biya wanda har yanzu hakan bai samu ba tukunna.
A daya bangaren shi kuma Dangote yana bukatar farashi wanda babu tallafi a cikinsa, saboda ya samu ya tace ya sayar da shi a kasuwa bisa alkaluman da sukayi dai dai da kasuwa.
A karshe mai sharhin kan sha’anin tattalin arziki na yau da kullum ya bayyana cewa mafitar itace gwamnati ta dauki matakai masu inganci wajen dai-daita wadan nan bukatu na kowani bangare ta hanyar samar da sauki da kuma adalci.
A yayin da matatar man ke shirin samar da kayayyaki iri-iri da suka hada da sinadarai na man fetur, Dangote ya bayyana irin tasirin da ake samu a fannin tattalin arziki, inda ya ce matatar za ta kawar da bukatar Najeriya na shigo da albarkatun man fetur daga kasashen waje.
Har yanzu dai ‘yan Najeriya na cigaba da zura ido wajen ganin yadda zasu samu saukin rayuwa ganin cewa yanzu kasar ta sami babbar matatar mai amma kuma farashin mai na kara hauhawa, rayuwa kuma na kara tsada.
-Yusuf Aminu Yusuf
Dandalin Mu Tattauna