Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Mai Ta Dangote A Najeriya Na Samar Da Albarkatun Man Fetur A Kasuwannin Cikin Gida


Kamfanin matatar man Dangote
Kamfanin matatar man Dangote

A ranar Talata ce matatar man Dangote ta Najeriya ta fara samar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida, in ji wani babban jami’in kamfanin da kungiyoyin sayar da man fetur, wani muhimmin mataki a yunkurin da kasar ke yi na samun dogaro kai a fannin makamashi.

An gina matatar man, wadda ita ce mafi girma a nahiyar Afirka, a wani yanki da ke wajen babban birnin kasuwanci na Legas, hamshakin attajirin nahiyar, Aliko Dangote ne ya gina ta, a kan kudi dalar Amurka biliyan 20 kuma an kammala ta ne bayan shafe shekaru da dama da aka fuskanci jinkiri.

Zata iya tace ganga 650,000 a kowace rana (bpd) kuma zata kasance mafi girma a Afirka da Turai idan ta kai ga cikakken karfinta a wannan shekara ko shekara mai zuwa.

Crude oil tanker Otis delivers crude oil for Dangote Refinery in Lagos
Crude oil tanker Otis delivers crude oil for Dangote Refinery in Lagos

Shugaban ma’aikatar Dangote, Devakumar Edwin, ya tabbatar da jigilar man dizal da na jiragen sama zuwa kasuwannin cikin gida.

‘Yan kasuwar man na gida sun amince da farashin Naira 1,225 wanda ya yi kasa dalar Amurka 1 a kowace litar dizal bayan wata yarjejeniya da suka kulla, in ji Abubakar Maigandi, shugaban kungiyar masu kasuwancin fetur mai zaman kanta ta Najeriya.

ALIKO DANGOTE
ALIKO DANGOTE

Mambobin kungiyar suna mallakar gidajen sayar da fetur kusan 150,000 a fadin Najeriya, inji Maigandi.

Kungiyar dillalan da kananan rumbun ajiyan mai ta Najeriya, ta ce mambobinta na neman takardar lamuni domin sayen man fetur daga hannun Dangote.

“Mambobin mu suna tattaunawa da bankuna kuma wannan tattaunawa ta kai nesa, idan muka samu takardun banki, za mu fara daukar kayayyakin,” in ji sakataren zartarwa na kungiyar Femi Adewole.

Ana dai kyautata zaton matatar man Dangote a matsayin wadda zata kawo karshen dogaron da Najeriya ke yi kan kayayyakin man fetur da ake shigowa da su daga kasashen waje. Najeriya ita ce kasa mafi yawan al'umma a Afirka, kuma ita ce kan gaba wajen hako mai, amma duk da haka tana shigo da kusan dukkan man da take amfani da shi saboda rashin matatu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG