Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kyari Ya Kalubalanci Dangote Ya Bayyana Sunan Jami’in NNPC Dake Da Hannu A Matatar Man Fetur A Malta


Malam Mele Kyari Shugaban NNPC
Malam Mele Kyari Shugaban NNPC

A sakon daya wallafa a shafinsa na X a yau Talata, Kyari, ya bukaci shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya fito fili ya bayyana sunan jami’in NNPC daya mallaki masana’antar tace albarkatun man fetur a kasar Malta.

Shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari, yace bai mallaki kamfanin sarrafa man fetur a kasar Malta ba, sannan bai san wani daga cikin jami’an kamfanin daya mallaki irin wannan masana’anta a kasar dake kan tsibiri a nahiyar Turai ba.

A karshen makon daya gabata, Dangote, yace wasu jami’an kamfanin NNPC da dillalan man fetur na gudanar da wata masana’antar sarrafa albarkatun man fetur a Malta, don haka suke kokarin hana tace albarkatun man a gida Najeriya.

A martanin daya mayar a yau Talata, Kyari yace, “domin fayyace zarge-zargen da aka yi game da masana’antar sarrafa albarkatun mai, bana mallaka ko gudanar da kowane irin kasuwanci a ko’ina a fadin duniya kai tsaye ko ta hanyar amfani da wasu in banda gonar da nake nomawa.

"Haka kuma bani da masaniya game da wani jami’in kamfanin NNPC, daya mallaka ko yake gudanar da masana’antar sarrafa albarkatun man a kasar Malta koma wani wuri a duniya.

“Kamfanin tace mai a Malta ko wani bangare na duniya bashi da tasiri akan harkokin kasuwanci ko gudanarwar kamfanin NNPC.”

“Domin kore shakku, zamu yi amfani da dokokinmu na tabbatar da da’a wajen bankado irin wannan jami’i, in akwaishi, kuma ni da kaina zan bada shawarar a fallasa shi tare da mikashi hannun hukumomin tsaro domin daukar matakan da suka dace ”.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG