Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Man Dangote Ta Fara Sarrafa Man Fetur


Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)
Matatar mai ta Dangote (Hoto: Facebook/Dangote)

Matatar man Dangote ta Najeriya ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan, in ji wani jami'in gudanarwa a ranar Litinin kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ruwaito.

Matatar man da ta kai dala biliyan 20 da aka gina a wajen birnin Legas, wacce hamshakin attajirin nan ‘dan Najeriya, Aliko Dangote ya gina, ta fara aiki ne a watan Janairu tare da samar da kayayyakin da suka hada da na fita da man jiragen sama.

Ita dai matatar man mai fitar da ganganr mai 650, 000 a kowacce rana kuma mafi girma a Afirka an yi alkawarin za ta saukaka tsadar mai da kuma dogaro da man da ake shigowa da shi daga kasashen waje cikin Najeriya.

"Muna gwada samfurin (man fetur) kuma daga baya zai fara kwarara cikin tankunan da ake samarwa," in ji Devakumar Edwin, mataimakin shugaban kamfanin Dangote Industries Limited.

Sai dai bai bayyana takamaiman lokacin da man fetur din zai fara shiga kasuwannin kasar ba.

Edwin ya ce kamfanin mai na kasar NNPC Ltd, mai shigo da mai a Najeriya shi kadai za a sayar wa man fetur kadai.

"Idan har kuma babu wanda ke sayan shi, za mu fitar da shi zuwa kasashen waje kamar yadda muke fitar da man jiragenmu da dizal," in ji Edwin.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG