Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Bukaci A Dakatar Da Shugaban Hukumar NMDPRA


Injiniya Farouk Ahmed - NMDPRA
Injiniya Farouk Ahmed - NMDPRA

Majalisar Wakilai ta yi kira ga Gwamnatin Tarraiya da ta dakatar da Shugaban Hukumar Kula da harkar man fetur ta Najeriya har sai an kammala binciken zarge-zargen da ake yi wa abinda ta kira "kalamai mara dadi da zai iya kashe wa kasar kasuwa" da shugaban hukumar ya yi.

Shugaban hukumar ta man fetur dai yayi kalamai ne kan matatan man Dangote a 'yan kwanakin nan.

Aliko Dangote
Aliko Dangote

Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa mai muhimmanci ga jama'a, wanda 'dan majalisar wakilai daga jihar Edo, Esosa Iyawe ya yi.

Dan majalisa Esosa Iyawe ya jaddada cewa bincike ya zama dole domin an yi zargin hukumar kula da Man Fetur wato NMDPRA a karkashin shugabancin Malam Farouk Ahmed tana bada lasisi ga wasu 'yan kasuwa da ke shigo da gurbataccen man dizil cikin kasar, wanda ake ganin yana dauke da sinadarin sulfur da ya wuce 1800ppm da 2000ppm.

Iyawe ya ce irin wannan dizil yana haifar da babbar illa ga lafiya da gurbace injinan motoci kuma haka yana kawo wa 'yan kasa asarar kudi.

Iyawe ya ce Farouk ya yi zargin cewa Matatar Man Dangote ita ce ta ke bada irin wannan man dizil 'din shi yasa Majalisa za ta yi binciken kwakwaf domin gane gaskiya.

Matatan man Dangote
Matatan man Dangote

A nasa jawabi 'Dan majlisa Sagir Ibrahim Koki ya yi karin haske kan irin binciken da Majalisar za ta yi, inda ya ce majalisa za ta yi bincike har iri 30 ciki har da batun matatun mai a Najeriya da aka ce ba sa samun isashen danyen mai da za su tace shi yasa basa aiki.

Sagir ya ce za su yi binciken zargin da aka yi akan Matatar Man Dangote kuma tuni har an riga an aika da wasikun gayyata ga wadanda abin ya shafa da kuma masu ruwa da tsaki a harkar mai.

To sai dai Sanata mai wakiltan jihar Nasarawa ta Yamma Ahmed Aliyu Wadada yana mai ra'ayin cewa wanda ya yi zargi kan matatan man Dagote ya kamata a kama shi, domin ko mutum baya son Dangote, ko mutun baya son addinin Dangote, dole ne in dai kana mai kishin Najeriya, dole ne ka jinjina wa Dangote saboda Dangote yayi rawar gani a fannin kasuwanci.

ALIKO DANGOTE
ALIKO DANGOTE

Wadada ya ce dole ne Majalisar ta tashi tsaye domin a yi bincike na kwakwaf saboda a kwato wa kasa 'yanci domin in an yi sa'a za a samu manyan 'yan kasuwa su shigo wannan kasa su zuba jari.

Shi kanshi shugaban hukumar kula da man fetur Farouk Ahmed ya yi bayani yana cewa yana neman a yi masa uzuri a fahimci abinda yake nufi da bayanan da yayi.

Farouk ya ce a yi hakuri a san yanayin shugabanci da abinda ya kunsa kafin a dauki mataki, domin tsari ne da ake yi a ma'aikatar da yake shugabanta. Farouk ya ce yana gudun kar wani abu ya faru nan gaba, a koka da ma'aikatar sa.

An dai ba kwamitin Majalisar Wakilai da ya fara binciken zargin da aka yi kan batun shigo da gurbatatcen dizil makonni 4 domin ya kammala aiki.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar Da Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur Akan Kalaman Da Ya Furta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG