Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ingancin Manmu Zai Iya Gogayya Da Na Ingila, Amurka - Dangote


Aliko Dangote
Aliko Dangote

“Da zarar mun kammala wasu tsare-tsare da kamfanin NNPCL, man mu zai fara shiga kasuwa.”

Bayan fiye da shekara guda da kaddamar da ita a watan Mayun 2023, a yau Talata matatar man Dangote, ta fitar da kason farko na man fetur, daga matatar daka iya tace ganga dubu 650 a kowace rana.

A yayin wani taron manema labarai, hamshakin attajirin nan kuma mamallakin matatar man, Aliko Dangote, ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar “yanzu ne za su fara samun ingantaccen man fetur”.

A cewar Dangote, “ingancin manmu zai iya yin gogayya da na Ingila da Amurka da na ko’ina a fadin duniya. Za mu tabbatar cewa babu wanda ya dara a bangaren inganci.”

Mamallakin matatar man ta Dangote ya kara da cewa, da zarar kamfaninsa ya kammala wasu tsare-tsare da babban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), man zai isa kasuwa.

“Da zarar mun kammala wasu tsare-tsare da kamfanin NNPCL, manmu zai fara shiga kasuwa.”

A jiya, Litinin ne wani jami'in gudanarwar kamfanin ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa matatar man Dangote ta fara sarrafa man fetur bayan tsaikon da aka samu sakamakon karancin danyen mai a baya-bayan nan,

"Muna gwada samfurin (man fetur) kuma daga baya zai fara kwarara cikin tankunan da ake samarwa," in ji Devakumar Edwin, mataimakin shugaban kamfanin Dangote Industries Limited.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG