Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Man Dangote Ta Dage Shirin Samarda Man Fetur Zuwa Tsakiyar Watan Yuli


Matatar Man Dangote
Matatar Man Dangote

Shugaban Matatar Man, Aliko Dangote, ya alakanta sauyin lokacin da aka samu da wani dan tsaiko saidai ya baiwa al’umma tabbacin cewar man fetur zai shiga kasuwa a tsakanin mako na 2 zuwa na 3 ga watan Yulin.

Matatar man Dangote dake Legas ta dage lokacin data tsayar domin fara samarda man fetur daga watan Yunin da muke ciki zuwa tsakiyar watan Yuli mai kamawa.

Shugaban Matatar Man, Aliko Dangote, ya alakanta sauyin lokacin da aka samu da wani dan tsaiko saidai ya baiwa al’umma tabbacin cewar man fetur zai shiga kasuwa a tsakanin mako na 2 zuwa na 3 ga watan Yulin.

Dangote ya bayyana hakan ne sa’ilin daya karbi bakunci wata tawagar sanatoci karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, dake rangadin duba matatar da aka gina a Legas akan dala biliyan 20 a Lahadin data gabata.

A ruwaito Dangote na cewar, “mun samu dan tsaiko amma man fetur zai fara samuwa tsakanin 10 zuwa 15 ga watan Yuli mai kamawa amma zamu kyale shi a tanki domin ya kwanta, daga nan kuma zamu iya mika shi zuwa kasuwa.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG