Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Matukar Damuwa Game Da Yanayin Ba Da Agaji A Garin Goma Na Kasar Congo - MDD


Fada da kashe-kashe ya sa mutane kauracewa gidajensu daga garin Goma na Congo zuwa sansanan ‘yan gudun hijira na Gisenyi, Jan. 28, 2025.
Fada da kashe-kashe ya sa mutane kauracewa gidajensu daga garin Goma na Congo zuwa sansanan ‘yan gudun hijira na Gisenyi, Jan. 28, 2025.

A yau Talata MDD tace akwai matukar damuwa dangane da yanayin bada agaji a garin Goma na Jamhuriyar Congo da aka yiwa kawanya, ganin yawan mutanen da aka raba da muhallansu, ga karancin abinci da satar kayan agaji da ambaliya ga asibitoci na marasa lafiya da kuma yadda fyade ya zama ruwan dare

Hukumomin bada agaji sun yi gargadin cewa hare-haren da ake kaiwa kan kayayyakin samar da ruwan sha da hasken lantarki na iya sabbaba barkewar miyagun cututtuka irinsu kwalara, inda suka kara da cewa fadan da ake gwabzawa a kusa da wani dakin binciken kimiya da ke garin na iya sanadiyar kubucewa tare da yaduwar kwayoyin cuta irinsu Ebola.

Garin Goma, Congo
Garin Goma, Congo

“Akwai matukar damuwa game da yanayin bada agaji a kewayen garin goma,” kamar yadda mai magana da yawun hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya (OCHA), Jens Laerke ya shaidawa manema labarai a Geneva.

Ya kara da cewar abokan aikinsu na MDD sun bada rahoton “harbe-harben manya da kananan bindigogi da makaman atilare a fadin birnin, tare da barin dimbin gawawwaki akan tituna”.

Garin Goma, Congo, Jan. 28, 2025
Garin Goma, Congo, Jan. 28, 2025

Ya ce takwarorinsu na Majalisar Dinkin Duniya suna ba da rahoton "mummunan harbe-harbe da bindigogi a fadin birnin, da kuma kasancewar gawarwaki da dama a kan tituna".

Birnin mafi girma a gabashin jamhuriyar Dimokiradiyar Congo ya zamo filin daga tun bayan da kungiyar ‘yan tawayen M23 karkashin jagorancin ‘yan Tutsi da sojojin Rwanda suka shiga tsakiyar Goma a daren Lahadin data gabata bayan shafe tsawon makonni suna kara tunkararsa daga sassan yankin.

Binciken mutane masu tserewa daga garin Goma na Congo akan iyakar Gisenyi, Rubavu gundumar, Rwanda, Jan. 28, 2025.
Binciken mutane masu tserewa daga garin Goma na Congo akan iyakar Gisenyi, Rubavu gundumar, Rwanda, Jan. 28, 2025.

Hare-haren da ake kaiwa cikin sauri wata babbar alama ce ta kazancewar yaki a yankin gabashi na faffadar kasar tsakiyar Afrika mai arzikin ma’adinai, wacce ke fama da yaki tsakanin kungiyoyi masu dauke da makamai dake samun goyon bayan abokan hammayar yankin tun bayan kisan kiyashin Rwanda na 1994.

Rikicin ya kuma haifar da tabarbarewar ayyukan bada agaji, tare da tursasawa mutane fiye da rabin milyan barin gidajensu tun a farkon shekarar da muke ciki, kamar yadda alkaluman mdd suka bayyana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG