Luguden wutar makaman atilare ta girgiza birnin goma dake gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Kongo da safiyar yau Litinin, yayin da kasar Faransa ke gargadin cewar birnin dake zama cibiyar yankin mai arzikin ma’adinai na daf da fadawa hannun ‘yan bindiga da dakarun Rwanda.
A daren jiya lahadi ne kungiyar ‘yan tawayen M23 mai gwagwarmaya da makamai da sojojin Rwanda suka kutsa kai zuwa tsakiyar birnin Goma bayan shafe makonni suna tunkararsa daga lardin Kivu na Jamhuriyar Dimokiradiyyar Kongo.
Birnin, dake daura da kan iyakar Rwanda, ya kasance mazauni ga mutum fiye da milyan guda da ‘yan gudun hijirar da adadinsu ya kusa kai hakan, a yankin dake fama da rikicin cikin gida dana ketaren kan iyaka tsawon shekaru 30.
Fadan baya-bayan nan ya sake tabarbara rikicin bada agaji, inda ya raba fiye da mutane 400, 000 da gidajensu tun daga farkon shekara, a cewar Majalisar Dinkin Duniya.
A sanarwar data fitar a daren jiya Lahadi, kungiyar M23 tayi ikirarin cewar “yau madaukakiyar rana ce dake zama alamar ‘yanta birnin goma, “ inda ta baiwa sojojin Kongo wa’adin mika makamansu.
Daruruwan mutane ne suka yi yunkurin tserewa daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo zuwa Rwanda a jiya Lahadi, yayin da aka yi ta harbe-harbe a gabashin birnin da ke da nisan kilomita kadan daga fagen daga.
Bintu Keita, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman a kasar Congo, ta shaidawa wani taron gaggawa na kwamitin sulhu na MDD a jiya Lahadi cewa, al'amura a birnin na Goma sun dagule.
“Dakarun M23 da na Rwanda sun kutsa cikin Munigi da ke wajen birnin Goma, lamarin da ya haifar da firgici ga jama’a. An toshe hanyoyi kuma ba za a iya amfani da filin jirgin ba don gudun hijira ko ayyukan jin kai. Kungiyar M23 ta sanar da rufe sararin samaniyar Goma. Wato mun makale.”
Dandalin Mu Tattauna