Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Shigar Da Kara Sun Bukaci A Yankewa Membobin M23 Hukuncin Kisa


Mayakan M23
Mayakan M23

Wani mai shigar da kara a Congo ya bukaci wata babbar kotu a Kinshasa ta yanke hukuncin kisa a kan wasu mutane 25 da ake tuhuma da zama membobin kungiyar ‘yan tawayen M23

Mai gabatar da karar ya bukaci a daure wani mutum na 26 a gidan yari na tsawon shekaru 20.

Tun daga karshen shekara ta 2021 kungiyar 'yan Tutsi ta M23 da ke samun goyon bayan Rwanda ta kwace yankuna da dama a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.

Mutum biyar ne kawai daga cikin wadanda ake tuhumar ke halartar shari’ar a kotun soji, sauran kuma ana zaman na kotun ne a bayansu. Suna fuskantar tuhume-tuhume na laifukan yaki, da hannu wajen tayar da kayar baya da kuma cin amanar kasa.

Wanda ya fi fice daga cikin mutanen da ake tuhuma shi ne Corneille Nangaa, tsohon shugaban hukumar zaben kasar Congo. A watan Disamba ya ba da sanarwar a Nairobi cewa an kafa kungiyar Fleuve Congo (AFC), kungiyar siyasa da ayyukan soji ta kungiyoyin 'yan tawaye ciki har da M23.

Ana tuhumar wasu manyan jiga-jigan kungiyar ta M23 da suka hada da shugabanta Bertrand Bisimwa da shugaban soji Sultani Makenga da kakakinta Willy Ngoma da Lawrence Kanyuka. Sai dai babu daya daga cikin mutane biyar da ake tuhuma a kotun da aka sani sosai.

Biyu sun yarda cewa su membobin kungiyar AFC ne. Daya daga cikinsu mai suna Nkangya Nyamacho wanda ake yi wa lakabi da ‘Microbe’ ya shaida wa kotun cewa, ya koma AFC ne saboda akwai rashin adalci da wariya a kasar nan.

Wanda ake karar da aka bukaci a yanke masa hukuncin zaman gidan yari, ya ci gaba da cewa, ba shi da laifi, yana mai cewa an kama shi ba bisa ka’ida ba saboda sunansa Nangaa.

An fara shari’ar ne a makon da ya gabata da wasu mutane 25 da ake tuhuma, inda 20 daga cikinsu ke gudun hijira, amma kuma an tuhumi tsohon kakakin kungiyar M23.

Ana sa ran lauyoyin wadanda ake kara za su gabatar da hujjojin kariyar su yau Talata.

A cikin watan Maris, gwamnatin Kongo ta yi fatali da sukar da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi, tare da dage hukuncin kisa da aka yi tun shekara ta 2003, da nufin kai hari kan jami'an soji da ake zargi da cin amanar kasa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG