Wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji sama da 270 ya kife a wani kogi kusa da Kinshasa babban birnin kasar Kongo, inda sama da mutane 80 suka mutu, in ji shugaban kasar, Félix Tshisekedi, jiya Laraba.
Wannan dai shi ne mummunan hatsarin kwale-kwale na baya-bayan nan da ya auku a kasar da ke tsakiyar Afirka.
Sanarwar da Tshisekedi ya fitar ta ce, jirgin ruwan da aka kera a cikin gida ya kife da yammacin ranar Litinin a lardin Maï-Ndombe da ke gabar kogin Kwa.
Kwale-kwalen na dauke da fasinjoji 271 zuwa birnin Kinshasa a lokacin da ya lalace kuma yana dauke da lodi fiye da kima, kamar yadda Ren Maker, kwamishinan ruwa na gundumar Mushi inda hatsarin ya afku, ya fadi.
Maker ya ce mutane 86 daga cikin fasinjojin sun mutu yayin da 185 suka samu yin iyo zuwa gabar teku, mai tazarar kilomita 70 (mil 43) kusa da birnin Mushie mafi kusa.
Dandalin Mu Tattauna