Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zafafa Fada Tsakanin Dakarun Congo Da Na 'Yan Tawaye


Congo Violence
Congo Violence

Zafafar wannan fadan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi, da na Rwanda Paul Kagame za su gana a yau Lahadi a kasar Angola, wadda ke shiga tsakani a rikicin.

Rundunar sojin kasar Congo ta bayyana cewa, fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin kasar da kungiyar 'yan tawayen M23 ya yi kamari a gabashin kasar ta Congo a cikin 'yan kwanakin nan, gabanin tattaunawar zaman lafiya da ake sa ran za’a yi a yau Lahadi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, rundunar sojin Congo ta zargi ‘yan tawayen na M23 da kashe fararen hula 12 a farkon makon nan, a kauyukan yankin Lubero da ke lardin North-Kivu a gabashin kasar.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta ‘yan tawayen ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa, kungiyar ta musanta zargin, yana mai bayyana zargin a matsayin "farfaganda" daga gwamnatin Congo.

Kungiyar ‘yan tawayen M23 na daya daga cikin kungiyoyin masu dauke da makamai kimanin 100 da ke fafutukar neman mafaka a gabashin Congo mai arzikin ma'adinai da ke kan iyaka da kasar Rwanda, a wani rikicin da ya haifar da daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya. Sama da mutane miliyan 7 ne suka rasa matsugunansu.

Kasar Congo da Majalisar Dinkin Duniya sun zargi Rwanda da marawa kungiyar ‘yan tawayen baya. Rwanda ta musanta wannan ikirarin, amma a watan Fabrairu ta amince cewa tana da sojoji da tsarin makamai a gabashin Kongo don kiyaye tsaronta.

Zafafar wannan fadan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Congo Felix Tshisekedi, da na Rwanda Paul Kagame za su gana a yau Lahadi a kasar Angola, wadda ke shiga tsakani a rikicin. Wannan ce ganawarsu ta farko a hukumance tun daga shekarar bara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG