WASHINGTO, D.C. - An dauki sama da sa'o'i 30 ne kafin sojojin Somaliya suka iya kakkabe mayakan da suka kutsa kai cikin otel din Hayat na Mogadishu a yammacin Juma'ar da ta gabata, a wani harin da suka fara da fashewar abubuwa masu karfi.
"A yayin harin, jami'an tsaro sun ceto fararen hula da dama da suka makale a otal din, ciki har da mata da yara," in ji kwamishinan ‘yan sanda Abdi Hassan Hijar, ya shaida wa manema labarai.
Har yanzu ‘yan sanda ba su bayar da cikakken bayani kan yadda harin ya auku ba, kuma ba a san adadin ‘yan bindigan da suka shiga otal din ba.
Otal din Hayat wani shahararren otal ne kusa da hedkwatar Sashen Binciken Laifuka na Somaliya a tsakiyar birnin.
Wani jami’in ‘yan sanda ya shaidawa Muryar Amurka ta wayar tarho a ranar Asabar cewa hukumomin tsaro na da hannu wajen ceto fararen hula da suka makale a otal din.
A dai wannan kazamin harin an kashe akalla mutane 20 tare da jikkata wasu da dama.
AP/REUTERS