Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Somalia Sun Yi Fito Mu Gama Da Mahara a Mogadishu


Jami'an tsaron Somalia
Jami'an tsaron Somalia

Jami’an tsaro a kasar Somaliya sun gwabza fada da mahara na tsawon sama da sao’i hudu a jiya Lahadi wanda ya kawo karshen hari da mamaye otel din dake gabar ruwa.

Ismail Muktar kakakin ma’aikatar yada labarai, ya fadi cewa mutane 11 aka kashe, da suka hada da jami’in tsaro daya. Ma’aikatan motar daukar marasa lafiya sunce sun dauki kusan mutane 30 da suka ji raunuka.

Jami’ai da wadanda abun ya faru a ganin idonsu sun bayyana wa VOA cewa daf da karfe shida na yammaci ne dan kunar bakin wake a cikin mota ya tada bom a kofar fitaccen otel din Elite, Lido, da ke bakin taku a Mogadishu. Jim kadan sai yan bindiga 4 suka farma otel din.

An harbe aka kuma kashe dukan maharan hudu, a cewar Muktar.

Sojojin sun ceto sama da mutane dari biyu daga otal, ciki har da mai otal din, Abdullahi Mohamed Nur, dan majalisa kuma minista.

Mayakan kuniyar al-Shabab sun dauki alhakin kai harin.

Shugaban kiungiyar ‘yan jaridar Somalia, Mohamed Ibrahim Moalimuu, yana cikin mutanen da suka shedi lamarin, yayin da suke zaune a wajen otal din lokacin da fashewar ta uku.

Ya fadawa Muryar Amurka cewa sun isa otel din da mintuna 15 kafin fashewar tare da abokin sa Abdirazak Abdi Abdullahi, ma’aikcin gidan radiyon gwamnatin kasar. Maharan sun kashe Abdullahi bayan da suka yi harbin farko, inji Moalimu a hirarshi da Muryar Amurka,

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG