Ba tare da bada cikakken bayani ba, ma’aikatar ta Pentagon ta fada a wata ‘yar takaitacciyar sanarwa cewa “za a kwashe galibin” dakarun Amurka da kaddarori a Somalia zuwa farkon shekarar 2021.
Akwai kimanin sojoji 700 a kasar da ke gabashin Afrika, wadanda ke bada horo da shawarwari ga sojojin Somalia a ci gaba da yakin da su ke yi da kungiyar masu tsattsauran ra’ayi ta al-Shabab, mai alaka da al-Qaida.
A kwanan nan Trump ya bada umurnin a rage yawan dakarun Amurka da ke Afghanistan da Iraq, kuma ya na sa ran janye wasu ko ma dukkan dakarun kasar da ke Somalia. Janar Mark Milley, shugaban hadakar manyan hafsoshin kasashen, ya fada a ranar Laraba cewa har yanzu ana kan yin muhawara game da makomar yawan sojojin Amurka a Somalia.
Matakin janye dakarun na Amurka daga Somalia da shugaba Donald Trump ya dauka yayin da kwanakinsa a matsayin shugaban kasa suka kusa karewa ya janyo bacin rai sosai daga ‘yan Somalia, wadanda a yau Asabar suka roki shugaba mai jiran gado ya sauya matakin.