Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Amurka Na Janye Sojojinta A Somalia Na Ci Gaba-Pentagon


Sojojin Amurka
Sojojin Amurka

Amurka na ci gaba da kwashe sojojinta daga kasar Somalia, biyo bayan umarnin shugaba Donald Trump a farkon wannan wata.

A cewar ma’aikatar tsaro ta Pentagon, jigrin ruwan sojin Amurka na USS Hershel yana gudanar da aiki a gabar tekun Somalia domin sake wa jami’an ma’aikatar tsaron Amurka wurin aiki daga Somalia zuwa wasu wurare daban a Afrika ta Gabas, a cewar mai magana da yawun rundunar hadin gwiwar Amurka da Afrika ta AFRICOM, Kelly Cahalan tana fada wa da Muryar Amurka.

Jirgin ruwan mai tsayin tsaku 800, dake tsaye a tungar sojin ruwan Somalia ta Souda Bay, Crete, zai taimakawa ayyuka daban daban na sojojijn ruwa, kamar taimakon ayyuka na musamma da kuma taimakon aikin jin kai, a cewar Sojin ruwa.

Umarnin na Trump wani bangare ne na neman janye sojojin Amurka a wurare da dama a duniya, ciki har da Afghanistan da Iraqi kafin ya fice daga shugabancin kasar a ranar 20 ga watan Janairu.

Kimanin sojoji Amurka 700 suke zaune a Somalia suna taimakawa jami’an tsaron kasar a yaki da kungiyar ‘yan ta’addan al-Shabab. Ana gudanar da aikin ba tare da lura da shi a cikin Amurka, amma dai yana cikin muhimman ayyukan da Pentagon ke yi na yaki da kungiyar al-Qaida a fadin duniya.

Pentagon ta ce sauya wa sojojin wurin aiki zai ci gaba da taimakawa yaki da ayyukan kungiyoyi masu tsaurin ra’ayi a yankin. Amma bata bayyana takamaiman yanda aikin zai gudana da kuma sanin adadin sojojin da za a sake musu wuri kuma yaushe ne za a kammala aikin sake musu wuri.

XS
SM
MD
LG